Za mu tallafawa wa ‘yan gudun hijira 3,400 da kiwon lafiya kyauta – Rundunar sojin sama.

0

Jami’in kula da kiwon lafiya na rundunar sojin sama ta Najeriya Azubuike Chukwuka ya bayyana cewa rundunar sa za ta tallafawa ‘yan gudun hijira 3,400 da kiwon lafiya musamman wadanda suka zaune a a kauyen Rann dake jihar Barno.

Ya fadi haka ne ranar Juma’a a taro da aka shirya don haka a garin Rann din.

Chukwuka ya ce sun tsara wannan shiri ne domin su inganta kiwon lafiyar ‘yan gudun hijira dake Rann wanda hakan ya sa suka zo wajen da kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya domin fara aiki gadan-gadan.

” Za mu kula da kiwon lafiyar mutane musamman mata da yara kanana kyauta a kauyen sannan za mu fadada haka zuwa wasu kauyukan nan gaba.

A karshe Muhammed Ibrahim mai shekara 65 da Chiroma Arima sun mika godiyar su ga rundunar sojin cewa a da sun kusa su rasa ganin su sai Allah ya kawo likitoci daga rundunar suka taimakawa a ganin su.

bada dadewa ba

Share.

game da Author