Jami’in hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC) Bello Ballama ya bayyana cewa daga yanzu hukumar za ta saka aiyukkan noma cikin hidimomin da dalibai za su rika yi wa kasa.
Ya ce yin haka zai taimaka wajen kawar da matsalar da ake samu na kin daukar dalibai a wasu ma’aikatu su ke yi.
” Za mu fara yin haka ne daga kan wadanda za su shiga sansanin horo na NYSC wato Batch ‘A’ Stream I a ranar 19 ga watan Afrilu.”
Ya kuma kara da cewa hukumar ta kebe filayen noma a duk fadin kasar nan domin dalibai masu yi wa hidima.
Daga karshe Ballama yace hukumar na iya kokarin ta wajen kawar da duk matsalolin da masu yi wa kasa kan yi fama da su.
Wadannan matsaloli sun hada da samun wurin yi wa kasa hidima, rashin samun wurin zama da sauran su.