Wasu likitoci a jami’ar Edinburgh dake kasar Scotland sun yi kira ga mutane musamman masu ciki da su guji shan magunguna ‘Panadol da Ibuprofen’ cewa hakan na iya kawo matsalar rashin haihuwa ga mai sha da ‘ya’yan da za a haifa nan gaba.
Likitocin sun gano haka ne a wata binciken da suka gudanar kan illolin da yawan shan wadannan magunguna ke yi wa lafiyar mace ko namiji, mata masu ciki da ‘ya’yan da suke dauke da su.
Likitocin sun ce binciken ya nuna cewa magungunan na rage yawan kwayayen haihuwa da ake samu a jikin mace ko namiji wanda hakan kan hana mutum haihuwa.
” Sai a ga macen da shekarun daina haihuwar ta bai kai ba amma ta daina haihuwa. Za kuma a iya gadon wannan matsalar idan iyayen suna yawaita amfani da wadannan magungunan.
“A dalilin sakamakon wannan bincike da muka gano ya sa muke kira ga mutane musamman mata da su yi dogon nazari kafin su hadiyi wani magani irin haka.”