Yau 1 Ga Watan Sha’aban -Sultan

0

Jiya ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa yau Laraba ce za ta kasance 1 Ga Sha’aban, 1439AH.

Sarkin Musulmin ya ce Laraba 18 Ga Afrilu, din ce za ta kasance ranar 1 Ga Sha’aban, wanda hakan ke nuni da cewa saura wata daya cif kenan a fara azumin watan Ramadan.

Wannan sanarwa ta fito ne daga wata takarda da Shugaban Kwamitin Shawara Kan A’amurran Addini Ga Sultan, Sambo Junaidu ya sa wa hannu.

Sa’ad Abubakar ya kuma yi addu’ar kara samun dawwamammen zaman lafiya da hadin kai a kasar nan.

Sha’aban shi ne wata na takwas, daga shi sai Ramadan, watan azumi.

Share.

game da Author