‘Yan sandan babban birnin Tarayya, Abuja, sun kama fitaccen dan gwagwarmayan nan Deji Adeyanju, a filin Unity Fountain, tare da dandazon ‘yan Shi’a da ke ci gaba da zanga-zangar kira ga gwamnati da ta saki shugaban kungiyar dake tsare fiye da shekara daya.
Ko da yake ba a san ainihin dalilan da yasa suka kama shi ba , sai dai ana ganin kamar don wani barambarabarma ne da yayi a gidan Talabijin din Channels inda ya bayyana cewa Buhari ya tafi asibiti ne ba taron kasashen rainon Ingila da za a yi a mako mai zuwa.
Tun bayan wannan hira, Kungiyar Masoya Buhari tayi kira ga jami’an tsaro da su Kama shi cewa yayi wa Buhari kazafi ne.
Deji ya sanar da kama shi ne ta sakon wayar tarho da ya tura mana a daidai an kama shi.