‘Yan sanda sun gayyaci Shehu Sani dangane da wani kisan da ake zargin ya na da masaniya

0

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna sun bayyana Shehu Sani a matsayin wanda ke da wata masaniyar wani kisa da aka aikata, wanda su ke kan bincike.

Dangane da haka ne sai Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar, Austin Iwar ya rubuta wa Sanata Shehu Sani wasika inda ya gayyace shi ya bayyana hedikwatar su a ranar 30 Ga Afrilu, 2018 domin a yi masa tambayoyi.

“Mu na gayyatar ka ne dangane da zargin masaniya da ka ke da ita, ta wani kisa da aka yi, wanda Rundunar Sojojin Najeriya ta Daya da ke Kaduna ta gabatar a gaban mu. An gabatar da wata shaida ta murya wadda a cikin maganganun da mai muryar ya yi, har da sunan ka ya ambata.” Wasu kenan daga cikin bayanan da wasikar da aka aika wa Shehu Sani ta kunsa.

PREMIUM TIMES HAUSA ta samu kwafen wasikar, wanda aka rubuta wa Sanata Sani da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya.

“Bayyanar ka za ta kara mana damar bai wa kowa hakkin sa da ‘yancin sa, sannan kuma hakan zai iya gaggauta kammaluwar binciken da mu ke yi a kan wannan al’amari.”

An aika wa Sanata Shehu Sani wakisar ce ta hannun Magatakardar Majalisar Dattawa, sannan kuma aka aika da kwafe daya na wasikar ga Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.

Sannan kuma ba a tabbbatar da ko wane rikicin da aka yi kisan ne ‘yan sanda su ka tsarma sunan Shehu Sani a ciki ba. Sai dai kuma a baya an sha yin gumurzu tsakanin magoya bayan sanatan da na gwamna Nasiru El-Rufai.

Wannan rikice-rikice ne ya haifar da barkewar rigar mutuncin jam’iyyar APC a jihar Kaduna, inda yanzu haka bangarori daban-daban kowane na kallon ta sa alkiblar daban da daya bangaren.

Shi kuwa Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Kaduna, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa batun ba shi da alaka da siyasa.

“Yanzu dai ba zan ce komai ba tukunna, domin mu na kan bincike.” Inji Kwamishinan ‘Yan sanda.

Iwar ya kara da cewa ba za a tsare Shehu Sani idan ya kai kan sa a ofishin su ba, domin idan su na son tsare shi, ai da sun kama shi sun tafi da shi tun a cikin majalisa.

Sai dai kuma Sanata Shehu Sani ya dora laifin neman sa da ake yi a kan gwamna El-Rufai, wanda ya ce dama tuni gwamnan ya gama shirya yadda zai kulla masa gadar sharri.

Ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa gwamnatin jihar Kaduna na amfani da ‘yan sanda domin su gina masa gadar sharri.

Ya ce makarkashiyar da gwamnatin ke kulla masa ta fito fili ne a cikin wasikar gayyatar da ‘yan sandan Kaduna ke yi masa wai ya bayyana domin a yi masa tambayoyi.

Ya kara da cewa tuni batun da ‘yan sanda ke neman sa domin su yi masa tambayoyi, ai ya na kotu. “Gwamnan ne ya rubuta wa alkalin kotun cewa ya na da ta sa bukatar a cikin lamarin shari’ar.” Inji Shehu Sani.

Share.

game da Author