‘Yan sanda da ‘Yan Shi’a sun sake yin fito-na-fito a Abuja

0

Bayan batakashin da akayi tsakani ‘Yan sanda da ‘Yan Shi’a a Babban Birnin Tarayya, Abuja ranar Talata da yayi sanadiyyar kama masu zanga-zanga sama da 100, a yau Talata ma rikici ya sake barkewa tsakani jami’an ‘Yan sandan da gungun ‘Yan Shi’a a daidai Kasuwar Wuse dake Abuja.

Wakiliyar mu da wannan arangama ya ritsa da ita ta bayyana mana cewa ‘yan Shi’a sun far wa ‘yan sanda bayan jami’an tsaron sun yi kokarin tarwatsa su.

Masu zanga-zangar sun yi amfani da duwatsu da sanduna suna jifar motocin ‘yan sandan a kokarin ci gaba da nuna fushin su da rike Shugaban Kungiyar Ibrahim El-zakzaky da gwamnati ke yi.

Mutane da ke gudanar da shagullan su sun fada cikin dimuwa da guje-guje, sai dai wani dan kasuwa ya fadi mana cewa cikin Kasuwar Wuse na nan kalau.

Share.

game da Author