‘Yan Majalisar dokokin Zamfara sun yi wa Hon Sa’idu jajen rasa iyalen sa 10

0

A ranar Litini ne wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara suka kai wa Honarabul Sa’idu Dambala ziyara sanadiyyar rasa iyalen sa 10 da ya yi a hadarin mota.

Iyalen Dambala wanda suka hada da ‘ya’yan sa hudu, jikoki uku, surikar sa daya tare da kawarta sun yi hadari ne a hanyar Gusau zuwa Sokoto ranar Lahadi inda dukan su suka rasu.

Kakakin majalisar dokokin jihar Sanusi Rikiji da ya jagoranci ziyarar ya ta’azantar da Dambala da ke wakiltar Bakura da ya dauki wannan al’amarin a matsayin gwaji ne daga Allah.

Share.

game da Author