‘Yan gudun hijira sun yi wa Gwamna Almakura ruwan duwatsu

0

A yau Talata ne wasu hasalallun ‘yan gudun hijira su ka jefi tawagar Gwamnan Jihar Nasarwa, Tanko Almakura da duwatsu.

Gwamnan da tawagar sa sun sha jifa ne a sansanin da ke garin Agwatashi, da ke cikin Karamar Hukumar Obi, a jihar Nasarawa.

Almakura ya kai ziyara ne a sansanin a lokacin da al’amarin ya faru. Ya je ne tare da shugabannin hukumomin tsaron jihar domin ya tantance al’amarin kisan da ya faru a yankin inda aka kashe mutane 32, kuma ake zargin cewa makiyaya ne suka yi kisan.

Yayin da gwamnan ya yi kokarin yi wa jama’a jawabi, sai wasu matasa a cikin sansanin suka fara wasu wake-waken bijirewa ga gwamnan, inda tilas gwamnan ya hakura ya fita bai yi jawabin ba.

Lamarin ya yi muni yayin da wasu matasan suka wuce-gona-da-iri, har suka fara jifar tawagar gwamnan da duwatsu, inda nan take sai da ‘yan sanda suka rika antaya musu barkonon tsuhuwa sannan aka tarwatsa su.

Da ya ke magana bayan ya sha ruwan duwatsu, Gwamna Almakura ya danganta lamarin da haushin irin rayuwar kuncin da hasalallun ke fama da ita a sansani.

“Na fahimci su na jin haushin irin zaman kuncin da su ke yi a sansanin ne, shi ya sa mu ka bi su da lalama. Domin idan na ce zan ci gaba da yi musu jawabi ma, ba zai sanyaya zukatan su ba, sai ma kara harzuka su.”

Sai dai kuma ya shawarci shugabannin yankin da su ja kunnen yaran na su. Ya na mai cewa amma kuma wasu matsalolin da yankin ke fama, su ne su ka jefa kan su a ciki.

“Matsawar yara matasa irin wadannan za su rufe shugabannin da jifa, to rikicin da ke faruwa a yankin kun san cewa akwai magana kenan.”

“Idan ka ce za ka dauki doka a hannun nka, to fa za a bar ka kai kadai ka je ka kare kan ka kenan.”

A karshe ya umarci shugabannin kakanan hukumomin da rikicin ya shafa da su bi su tantance yawan mutanen da rikicin ya yi wa illa domin a san irin tallafin da za a yi musu.

Share.

game da Author