Wasu ‘yan jagaliyar siyasa sun tarwatsa taron gangamin nuna goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abubakar Badaru su ci gaba da mulki a 2019.
An dai shirya taron ne a shiyyar Sanatan Arewa-maso-yamma, wato, Gumel, a filin wasa na garin jiya Lahadi, sai dai ya kare da hargitsin da tilas shugaban jam’iyyar APC na jihar, Ado Sani ya hakura bai yi jawabi a wurin ba.
’Yan dabar sun rika rera wakokin adawa dake da munanan kalamai, wadanda aka ce sun yi haka ne ga sanatan da ke wakiltar Gumel, Abdullahi Gumel, wanda dama sun hana shi hawan dakalin da masu jawabi ke hawa su na kamfe.
Tun da farko dama sai da aka yi wa sanatan shigar-burtu, sannan Sanata Danladi Sankara ya shiga da shi cikin filin taron, saboda gudun kada a ‘yan dabar su kai masa hari.
Sai dai kuma wasu na cewa wadanda suka hargitsa taron, magoya baya ne ga wanda ke son kwace kujerar daga hannun Abdillahi Gumel a zaben 2019.
An tsara cewa dukkan ‘yan majalisar tarayya da ke wakiltar jihar Jigawa da wakilan majalisar jiha, za su halarci taron, amma guda biyu kadai suka halarta.
Shi ma gabban bako Gwamna Badaru bai je ba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa duk wani mai rigar mutunci, musamman manyan ‘yan siyasa, sun rika sulalewa su na guduwa don kada ‘yan daba su ‘kaddamar’ musu.