Hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) ta bayyana cewa Najeriya ta sami saukin yaduwar zazzabin Lassa tun da aka shiga watan Afrilu.
Hukumar ta ce ta gano haka ne a ranar 15 ga watan Afrilu inda mutane biyar ne kawai suka kamu da cutar.
Bincike ya nuna cewa ta’adin da bullowar cutar ta yi a shekarar 2018 a Najeriya ta fi ta kowace shekara.
” Bana tun da cutar ta bullo mutane 400 ne suka kamu da cutar inda daga ciki 100 sun rasa rasu a tsakanin watannin Janairu da Faburairu’’