Yadda Sanatoci ke bushasha da kudaden garabasa

0

Wasu bayanai da PREMIUM TIMES ta ci karo da su, sun fallasa irin dimbin kudaden da sanatocin Najeriya ke karba.

Ga takaitaccen bayanin abin da takardar ta kunsa:

1. Su na kashe naira miliyan 1.8 a sayen jaridu kowane wata uku.

2. Kashe naira miliyan 10 zirga-zirga da sagarabtu a cikin Najeriya kowane wata uku.

3. Ana ware naira miliyan 1.5 kowane wata uku domin yi wa kwamfuta sabis.

4. Tsakanin 2011 zuwa 2015, kowa na karbar naira miliyan 45 duk bayan wata uku.

5. Tsakanin 1999 zuwa 2016 sanatoci 109 sun karbi naira biliyan 314 da kuwa wasu naira biliyan 53 a cikin mulkin Buhari duk a matsayin kudaden hidindimun yau da kullum.

6. Kowane Sanata na karbar naira miliyan 13.5 kowane wata, inji Sanata Shehu Sani a matsayin sallamar hidindimun yau da kullum.

7. Ana bukatar kowa ya rika bayyana yadda ka kashe na sa kudaden a kowane wata, amma ba su yin haka yadda ya dace.

8. Masu yi din ma akasari duk rasidan bogi ne su ke gabayarwa a Majalisar Tarayya. Kamar yadda majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES a Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Bayanan Bushashan wani Sanata da muka co Karo da:

A jadawalin bushashar wani Sanata an rattaba yadda ya burke naira miliyan 45 a cikin kwanaki 90 can baya cikin 2012.

Sanatan ya hau jirgin sama zuwa kasashen waje da naira milyan 8.

Ya kashe naira miliyan 10 a tafiye-tafiye nan cikin Najeriya a cikin kwanaki 90.

Ya kashe naira miliyan 7.4 wajen ‘biyan dan abin da ba a rasa ba.’

Har naira miliyan 3 ya kashe wurin yi wa ofis din sa kwalisa.

Naira miliyan 6.8 sun tafi wajen buga takardun bayanai.

Wato kowane sanata na karbar naira dubu 20 na sayen jarida a kowace rana. Jarida daya kuma naira N200 kacal ake sayar da ita. Da wuya a samu mai sayen guda biyar a rana daya.

Share.

game da Author