Yadda ministar Jonathan ta yi wa naira miliyan 450 rabon ’yan karta

0

A yau Litinin ne wata mai gabatar da shaida mai suna Annette Gyen, ta shaida wa mai shari’a a Babbar Kotun Tarayya da ke Jos, yadda tsohuwar Ministar Harkokin Ruwa, Sarah Ochekpe tare da wasu mutane biyu suka karkasa naira milyan 450 a cikin wani kankanin lokaci.

Zunzurutun kudin dai kamar yadda mai gabatar da shaida ta bayyana wa kotu, an ciro su ne daga cikin bankin Fedility, tare da Raymond Dabo da kuma Leo Jatau.

Dabo shi ne shugaban jam’iyyar PDP na jihar Filato a lokacin da aka kacaccala kudaden, yayin da shi kuma Jatau shi ne kodinata na yakin neman zaben Jonathan na jiahr Filato.

An bayyana cewa kudin wadanda aka cira farko 2015, sun fito ne daga hannun Ministar Harkokin Man Fetur, Dezani Alison-Madueke.

Hukumar EFCC ce ta maka su kotu, yayin da ta gabatar wa kotun shaidar cewa sun ci kudin kuma an cire kudin sabanin yadda dokar kasa wadda ta haramta harkalla da daka-dakar zamba ta 2012 ta shimfida.

Annette Gyen, wadda ma’aikaciyar bank ice, ta shaida wa kotu cewa ita dai ba ta ci ko sisi daga cikin kudin ba, domin ogan ta a bankin na Fedility a lokacin mai suna Martins Ezougbe ne ya umarci jami’an bankin su bayar da kudin ba tare da wata jikarar kaomai ba.

“Mu kuwa a ranar 25 Ga Maris, 2015, muka kira mutanen su uku, muka ba su kudaden.

“Bayan sun tabbatar da kudin sun cika cif-cif, suka ce mu ba su motar banki mai jigilar makudan kudade domin a loda musu loda kudin a ciki. Mu kuma mu ka bada mota domin a daukar musu.” Inji Anetta Gyen.

Ta ce baya ta haihu kuma labari ya sha bamban yayin da a ranar 8 Ga Janairu, 2017, sai ga wasika daga EFCC, inda aka nemi su yi cikakken bayanin yadda aka fitar da wadancan kudade da kuma wadanda aka bai wa su.

Ta ce sun maida wa EFCC amsa a ranar 10 Ga Janairu.

Wakilin NAN ya bayyana cewa mai gabatar da kara Ahmed Munchaka ya nemi kotu ta ba shi iznin gabatar da wasikun guda biyu a matsayin shaidu na farko.

Lauyoyin cewa suka yi bai kamata a gabatar da fotokwafe na wasikun a kotu ba, orijina ya kamata mai gabatar da kara ya gabatar.

Sai dai kuma an yi ta sa-toka-sa-katsi tsakanin mai gabatar kara da kuma lauyoyin Jatau da Dabo

A karshe dai Mai Shari’a Musa Kurya ya aza ranar 17 da 18 Ga Mayu, 2018 ranar da za a zartas da hukuncin za a iya karbar wasikun a matsayin shaida ko a’a.

Share.

game da Author