A taron da Kwamitin Zartaswa na APC ya gudanar a jiya Litinin, an amince cewa shugabannin jam’iyyar APC masu barin gado za su iya ci gaba da rike shugabancin jam’iyyar har tsawon shekara daya, kamar yadda aka gindaya a cikin Fabrairu, kafin Buhari ya bada shawara aka soke.
Hakan zai tabbata ne kawai muddin aka kasa gudanar da cikakken taron gangamin jam’iyya balle a sake zaben sabbin shugabanni.
An amince da wannan kudiri ne a jiya Litinin da rana, a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, bayan da Shugaban jam’iyyar APC na jihar Rivers, Ibiamu-Ikanya ya gabatar da wasu kudirori biyar, wadanda nan da nan Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya nemi a amince da su.
Hakan na nufin idan aka samu kiki-kaka da ja-in-ja a taron gangamin APC, har jam’iyyar ta kasa cika sharudda da dokoki na gudanar da zabuka, to shugabannin jam’iyyun na kasa, jiha da kananan hukumomi za su iya ci gaba har sai bayan an gudanar da zaben 2019 sannan su sauka.
Discussion about this post