TASHIN HANKALI: An sace amarya da kawayen ta 10 a Kaduna

0

Wani abin tashin hankali da ya auku a garin Birnin Gwari jihar Kaduna a daren Asabar shine yadda aka sace amarya sukutum da kawayen ta 10 a daidai a za a kai ta dakin mijinta.

Wannan al’amari ya tada wa mutanen garin Birnin Gwari hankali matuka.

Wani tsohon shugaban karamar hukumar Birnin Gwari, da baya so a fadi sunan sa, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES wannan abin tashin hankali da faru a garin.

Ya ce maharan sun tare motar dake dauke da amarya ne da kawayenta da kamar karfe 8 na dare.

” Yanzu dai abin ya zama ruwan dare a Birnin Gwari, kusan kullum sai kaji irin wannan tashin hankali. Muna rokon gwamnati ta taimakwa yan bangan.”

Share.

game da Author