TAMBAYA: Don Allah ina son Malam yayi mini Karin Bayani kan falalar Suratul Fatiha?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Suratul fataiha ita ce sura ta farko a cikin littafin Allah mafi girma, kuma sura mafi girma, an saukar da ita sau Biyu a Makka da Madina, ana karanta ta a cikin dukk sallar musulmi. Tanada Falala mai yawa, da Sirruka musu gamewa, tanada sunaye masu yawa.
ANA KIRANTA DA WADANNAN SUNAYE KAMAR HAKA:
1. Suratul Fatiha
2. Suratul Hamd
3. Suratush- Shifa’a
4. Suratul Munajat
5. Ummul- Kitab
6. Ummul- Qur’an
7. Fatihatul Kitab
8. Saba’ul Mathani
FALALAR SURATUL FATIHA
1. Ita ce Sura mafi girma a cikin littafi mafi al-farma wanda Allah bai saukar da irinta ba a duniya.
2. An saukar da Mala’ika da Bushara ga Annabi, yana cewa: Ka yi farinciki, da haske guda biyu: suratul Fatiha da ayoyi biyun karshen suratul Bakara. Babu wani Annabi da ya samu irinsu. Babu wani da zai yi roko dasu face anbashi abinda ya roka.
3. Babu Salla ga duk wanda Bai karanta suratul fatiha ba. Kuma a kwai sirri mai yawa gurin yawan maimaita ta acikn Salla.
4. Suratul fatiha ita ce mafi girman zikiri, ta kunshi zikirin Allah, godiya, yabo, da girmamawa.
5. Suratul fatiha tana maganin dukkan cutukan zuciya kamar Hassada, Girman Kai, Kyashi, takama da alfahari da sauran ciyukan zuciya.
6. Suratul fatiha tana maganin dukkan cutukan jiki da gabobi kamar zazzabi, ciwon kai, ciyon gabobi, da ciwukan ido, kunni da sauran kowane irin ciwo.
7. Suratul fatiha tana maganin cutukan Hauka, farfadiya, Jinnu da dukkan nau’in sihiri.
8. Suratul fatiha tana maganin Harbin kunama da cizon maciji da saura dabbobi masu dafi. Suratul fatiha tana bada kariya ga dukkan abinda mutum ke tsoro, (wato neman kariya ko tsari).
9. Ana karanta suratul fatiha don neman ko wace irin bukata da mutum yake da ita.
Amfani da Suratul Fatiha
1 – A karanta suratul fatiha karatu wuturi (wato sau daya ko uku, ko biyar, bakwai…) a tofa a ruwa, sai asha, ko ashafa, ko ayi wanka da shi.
2 – A karanta suratul fatiha karatu wuturi sai a tofa atafin hannu sai a shafa.
3 – A rubuta Suratul fatiha sai a wanke sannan sai asha, ko ashafa, ko ayi wanka da shi.
4 – A karanta suratul fatiha karatu wuturi sai ayi tawassuli da karatun kuma roki Allah.
5 – Yawan karatun fatiha yanada sirrin da Allah ne kwai ya barma kansa sani.
6 – A kwai wasu bukatu ko lalurori da sai anhada suratul fatiha da wasu ayoyi ko wasu ganyayyaki ko wasu sinadarai domin samun waraka ko biyan bukata.
Allah shi ne mafi sani
Ya Allah! Muna rokon ka arzikin duniya da lahira.
Imam Muhammad Bello Mai-Iyali
Harkatul Falahil- Islam
Barnawa Kaduna.
Discussion about this post