Masu zanga-zanga sun sace sandar mulkin Majalisar Dattawa

0

A safiyar yau Laraba ne masu zanga-zanga suka kutsa cikin zauren Majalisar Dattawa, suka tada hargitsin da har su ka sace sandar mulkin majalisa.

Ana kyautata zaton masu zanga-zangar magoya bayan Sanata Ovie Omo-Agege ne, wanda aka dakatar cikin makon da ya gabata saboda zakalkalewar da aka ce ya yi wajen zargin majalisa da kokarin kulla wa Shugaba Buhari gadar-zare ta hanyar yunkurin da aka yi na sauya ranakun gudanar da zaben 2019.

Wannan sandar dai ita ce alamar daraja da martabar Majalisar Dattawa, kuma ita ce tambarin karfin ikon majalisar.

Saidai kuma masu tasron majalisar sun shaida mana cewa wadanda suke dauke sandar mulkin sun taho majalisar ne tare da sanata Omo-Agege shine yasa muka kyale su su shiga majalisar.

Wadannan mutane sun kai su 10 sannan sun saka wannan sanda ne a cikin mota kirar jeep wat SUV suka yi tafiyar su.

Bayan haka majalisar ta soki wannan taargaza da sanata Agege yayi da kakkausar murya, inda tace hakan kamar shiri ne na yi wa majlisar juyin mulki.

Yayi kira ga jami’an tsaro da su mara wa majalisar baya sannan su fita farautar sanata Omo-Agege don ya dawo wa majalisar da sandar mulkin ta.

Share.

game da Author