Duk da amincewa da a sake zaben sabbin shugabannin jam’iyyar APC da jam’iyyar ta yi, Gwamnan jihar Adamawa Jibirilla Bindow ya ce shi ba za a yi sabon zaben shugabannin jam’iyya a Jihar sa ba. Na shi shafaffu da mai ne.
Jibirilla ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin jam’iyyar ta jiha suka kawo masa ziyara fadar gwamnati dake Yola.
Idan ba a manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci jam’iyyar ta gudanar da zabukkan kujerun shugabannin jam’iyyar na kasa da jihohi baki daya.
Jibirilla ya ce babu zaben da za ayi a jihar, cewa dukkan su a jihar suna nan daram dam a kujerun su.
” Wadanda za mu canza sune wadanda suka rasu amma duk wanda yake kai yanzu ya ci gaba da zama abin sa a kujerar sa.
Gwamna Bindow ya ce shi dama can yana tare da wadanda suke bayan kada a sake zaben shugabanni a jam’iyyar APC yanzu. A jihar sa ta Adamawa kuwa, babu wanda zai sauka da ga kujerar sa domin ” babu zaben da zan yi.” Inji Bindow.
Yanzu dai jam’iyyar na cikin wani irin sarkakiya ce domin har yanzu kan ‘ya’yan ta sun rabu game da zaben.