Shehu Sani na neman El-Rufai ya biya shi naira biliyan 5 ladar bata masa suna da yayi a radiyo

0

Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna ya maka Gwamnan jihar Nasir El-Rufai a Babbar Kotun Jihar, ya na neman diyyar naira biliyan 5 ladar bata masa suna da ya yi a gidan radiyo.

Idan za a tuna, shi ma El-Rufai ya maka Sanata Shehu Sani kotu, a cikin Fabrairu, ya na neman diyyar naira miliyan 500 shi ma.

To shi ma Sanata Sani, ya maka gwamnan kotu ne a ranar 20 Ga Afrilu, domin a bi masa abin da shi ma ya kira hakkin bata masa suna da ya yi.

Ya kuma nemi kotu ta tilasta wanda ya ke kara ko wani jami’in sa, ko ejan ko dan jagaliyar gwamnan da kada su kuskura su sake furta irin munanan kalaman batuncin da El-Rufai ya yi wa sanatan a gidan radiyon jihar.

Sannan kuma ya nemi kotu ta tilasta gwamnan rubuta wa sanatan takardar ban-hakurin ‘Allah-huci-zuciyar-ka.’

Har ila yau, Sanata Sani na so kotu ta tilasta wa El-Rufai yayata sanarwar janye kalaman da ya yi tare da bada hakuri a gidan radiyon da ya yi batuncin. Sani na so El-Rufai ya yi haka har kwanaki bakwai a jere.

Sannan ya kara neman kotu ta tilasta wa El-Rufai ya buga wannan takardar ban-hakuri a shafukan manyan jaridun kasar nan guda 4, kuma ya tabbatar ya buga su a shafukan da kowa zai iya gani ya karanta, kada a cusa sanarwar can a wani shafin da ba kowa ya damu da kai hankalin sa wurin ba.

Sanatan ya shaida wa kotun cewa kalaman da aka yada a kan sa, sun bata masa suna, sun sosa masa rai kuma sun keta masa rigar mutnci a idon jama’a, ta yadda furucin wanda aka yi da Hausa ya rage masa kwarjini a cikin al’umma.

Kalaman da Sanata Sani ke ikirarin an yi a kan sa dai an yi su ne a cikin watan Nuwamba, 2017, kuma ya kara da cewa tun bayan yi masa wancan kazafi, hakan ya janyo masa zubewar kimar da ya kwashe shekara da shekaru ya na ginawa domin kara wa kan sa daraja.

Sani ya ci gaba da cewa mummunan kazafin da El-Rufai ya yi masa ya zubar masa da mutunci, gaskiya da rikon amanar da ya shafe tsawon shekaru ya na gina wa kan sa. Ya ce duk wadannan kyawawan dabi’u da aka san shi da su, duk El-Rufai ya kifar da farantin da shi Sanatan ke tallabe da su a cikin rairayi.

Sanata Sani ya ce El-Rufai ya nuna shi a duniya a matsayin azzalumi, tantagaryar mahaukacin da ba mai iya warkar da shi da sauran munanan kalaman da suka sa sanatan har yau ya ke cikin halin damuwa, kunci, takaici, tozarci, wulakanci, tsangwama da kududun bakin cikin da ba zai iya misaltuwa ba.

Sanata Sani ya ce gwamnan ya yi masa mummunan kalaman ne saboda kin amincewa da aka ce ya yi na jihar Kaduna ta ciwo bashin dala milyan 350.

Share.

game da Author