SHARHI: Yadda ake rububin naira biliyan 100 kowace shekara a Majalisar Tarayya

0

Mai tafiya kan ci karo da inda gwamnati ta yi wasu ‘yan kananan ayyukan raya karkara, sai hankalin sa ko idanun sa kan kai ga wasu allunan da ke dauke da bayanin cewa: “Wannan aikin Sanata Wane ne ya daukin nauyin gina shi.”

‘Yan majalisar sun gwanance sosai wajen kakkafa wadannan sanbodin alluna, domin su nuna wa jama’a cewa su na aiki da kudaden da gwamnati ke ba su, domin gudanar da ayyukan a-gani-a-yaba a mazabun su.

Duk inda ka zagaya a fadin kasar nan, za ka rika ganin wasu allunan za ka gan su an kafa a inda a ke kan aiki, wasu a inda aka fara aikin aka watsar, wasu kuma a inda aka kammala aikin.

Daga baya-bayan nan, ana bai wa ‘yan majalisar naira biliyan 100 a kowace shekara domin su je gida su yi wa al’umma wasu ayyukan inganta al’umma, musamman ma a cikin karkara.

Sai dai kuma tun daga lokacin da aka fara raba musu wadannan kudade har yau, ana ta ‘yar-burum-burum, an ki a bayyana hakikanan gaskiyar yadda suke kashe kudade masu yawa haka.

PREMIUM TIMES HAUSA ta binciko yadda mambobin Majalisar Tarayya da na Dattawa su ke daka rububi kan kudin, yadda a karshe dai sai wadanda suka turo su wakilce kawai su ji a salansa. Sadoda wasu ayyukan kan kare ne da rabon garmar shanu ko ko injin markaden tattasai ga ‘yan jam’iyya ko ‘yan jagaliya, sauran al’ummar yankin kuwa, sai dain su ji a salansa.

Wadanne irin kudade ne wadannan?

Su ne kudaden da a Najeriya ake kira kudaden ayyukan raya mazabu da dan majalisa ko sanata zai bayyana wani aiki a mazabar sa, sai ma’aikata ko wata hukumar da abin ya shafa ta je ta yi aikin. Kuma a cikin kafasin shekara-shekara.

An shigo da wannan tsari ne tun farkon mulkin Olusegun Obasanjo, domin ana matsa wa sanatoci cewa su ina na su aikin?

Farko shigo da tsarin, ana bai wa Sanata naira milyan biyar, shi kuma dan majalisar tarayya na amsar naira milyan uku.

Da suka fasa suka ga jini ya fito, sai suka matsa wa Obasanjo lamba, har ya amince ya sa batun a cikin kundin dokokin kasar nan.

PREMIUM TIMES ta gano cewa a kan sa wuka ko zarto a gigara wa kudaden, a raba su gida biyu, wato Majalisar Dattawa na da kashi 40 bisa 100, yayin da Majalisar Wakilai ta Tarayya na da kashi 60 bisa 100.

A yankunan da aka samu aka dan lika musu wani aikin, da zaran an dan makala allo da sunan Sanata ko wakilin tarayya, to jama’ar yankin sai su dauka shi ne ya yi aikin da kudin aljihun sa, amma kuma ko sisi na shi babu a ciki.

Idan aka yi wannan kaso, sai kuma a zo a sake yin kashin dankali. Daga cikin naira biliyan 40 da ake ware wa Majalisar Dattawa, shugabannin majalisar su 9 ake ware wa naira biyan 20 a ce za a yi musu aiki ne da su a yankunan mazabun su. Sauran Sanatoci 100 kuma a karkasa musu aikin naira bilyan 20 kacal.

Su ma a Majalisar Wakilai ta Tarayya, ana ware naira bilyan 20 a ce na ayyukan da za a yi wa shugabannin majalisar ne a yankunan su. Sauran wakilai sama da 345 kuma su ke da naira bilyan 40.

Daga nan kuma sai a fara tunanin yadda za a raba ayyukan da za yi da kudaden a kowace shiyya na kasar nan. Amma a karshe yankunan Arewa ne aka fi bai wa kaso mafi kankanta idan aka yi la’akari da yadda ake kasa kudaden a tsarin shiyya-shiyya.

NAIRA MILIYAN 200 AKE WARE WA KOWANE SANATA

PREMIUM TIMES ta samu jin ta bakin Sanata Shehu Sani, wanda ya bayyana cewa:

“Shi wannan aiki da ake yi da kudaden da ake ware wa Sanatoci, ba wai kudaden ba ne ake ba su a hannun su. Za a ware wa kowane sanata naira miliyan 200 ne. Sai a ce to akwai kudin a hannun hukuma kaza, ka je ka kawo aikin da ka ke so a yi da kudin a shiyyar da ka ke wakilta. Idan ka je ka kawo ayyukan, to sai a je a yi aikin.”

YADDA AKE KARKATAR DA KUDADEN

Duk da cewa ba kudin ake dauka a damka wa ‘yan majalisar a hannun su ba, amma da ya ke Hausawa sun ce, ‘maso abin ka ya fi ka dabara’, su kan hada baki da hukumomin da kudaden ke hannun su wajen yi wa kwangila aringizon kara kudade fiye da yadda ya kamata a ce su aka kashe a ka yi aiki.

Ana kuma yin aringizon kudade kai tsaye a cikin wasu hukumomi. Misali, yawanci ‘yan majalisar tarayya da sanatoci sun fi yin ayyukan na su a karkashin Hukumar Samar da Kanana da Matsakaitan Masana’antu, wato SMEDAN. Amma abin mamaki, duk shekara sai an yi wa wannan hukuma aringizon bilyoyin kudade idan an kai kasafin kudi a gaban majalisa.

Ga wani misali, a shekarar 2017, SMEDAN da kan ta ta yi kasafin naira biyan 2.18. Amma sai majalisa ta yi mata aringizo, zuwa naira bilyan 9.52, wato abin da aka kara mata ya kai gaba dayan kasafin hukumar na shekara shida.

Ta nan ne ake karkatar da kudade da sunan wayar wa matasa kai, yi musu horon yadda za su kama sana’a, samar musu kayan gudanar da kananan sana’o’i ko kayan aikin wasu sana’o’in da sauran su.

To dalili kenan ba a iya kididdige aikin da aka yi da kudaden, saboda an karkatar da su wajenn gudanar da ayyukan da ba a iya ganin su a kasa, sai dai a kan takardar rasidi kawai.

Share.

game da Author