Shan kofin shayi sau uku a rana na kare mutum daga ciwon zuciya

0

Wasu likitoci a hukumar gudanar da bincike ‘Melbourne’s Baker Heart and Diabetes’ dake kasar Amurka sun bayyana cewa shan ganyen shayi ‘Tea’ ko kuma bakin shayi ‘Coffee’ kofi uku a rana na kare mutum daga kamuwa da cutar zuciya.

Likitocin sun ce sun gano haka ne bayan gudanar da bincike kan amfanin da sinadarin ‘Caffene’ (wanda ake samun sa a shayi) ke yi wa jikin mutum musamman wadanda ke fama da cutar ciwon zuciya.

” Mun gano cewa shan kofin shayi uku a rana ga mai fama da cutar zuciya yana rage illar da cutar ke yi a jikin sa sannan wadanda basu dauke da cutar idan har suna yin haka za su iya samun kariya daga kamuwa da wannan cuta.”

Jagoran wannan bincike Peter Kistler ya karyata camfin da mutane ke yi cewa wai masu fama da cutar zuciya bai kamata suna shan irin wannan shayi ba.

Kistler yace shan shayi musamman wanda ke dauke da sinadarin ‘Caffene’ ga wanda ke fama da irin wannan cuta zai taimaka masa wajen yadda zuciyar sa zata buga da kyau yadda ya kamata sannan ya kuma karfafa kaifin kwakwalwar mutum wajen fahimtar abubuwa.

A karshe Kistler ya yi kira ga mutane musamman masu fama da cutar zuciya da su dinga shan kofin shayi akalla sau uku a rana.

Share.

game da Author