SHAN INNA: Za a yi wa yara miliyan 1.6 alluran rigakafi a jihar Jigawa

0

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar Jigawa (JSPHCDA) Kabiru Ibrahim ya bayyana cewa hukumar za ta yi wa yara miliyan 1.6 ‘yan watanni 9 zuwa shekara biyar allurar rigakafin cutar shan inna a jihar.

Ya fadi haka ne da yake amsa tambayi daga manema labarai ranar Juma’a a Dutse sannan ya kara da cewa za su fara yin allurar ne daga ranar 7 ga watan Afrilu a kananan hukumomin jihar 27.

Ibrahim ya ce hukumar ta tanaji magunguna, ma’aikata da sauran ababen da za a bukata don ganin an sami nasarar gudanar da wannan aiki.

A karshe yayi kira ga iyaye, sarakunan gargajiyya,masu ruwa da tsaki a jihar da su mara wa hukumar baya don ganin an sami nasarar hakan.

Share.

game da Author