A karon farko a tarihin kasar, Saudiyya ta bude gagarimin taron mako guda na nunin kayan mata na kwalisar zamani, irin wanda kasashen Turai da Amurka su ka bai wa fifiko, wato ‘fashion parade.’
Za a shafe mako guda ana gudanar da bukin kalankuwar nunin kayan, inda tuni mata ‘yan kwalisa na kasar Saudiyya su ka fito kowace da gashin kan ta baki ya na sheki, da kuma matan kasashen Turai ta Gabas masu jajayen gashin kai suka cika babban zauren taro na otal din Ritz-Carlton Hotel da ke Riyadh, babban birnin kasar.
Matan duniya ‘yan kwalisa da dimbin wadanda suka shahara wajen yi wa mata kwalliya da gyaran jikin nan da aka fi sani da dilka, sun bayyana mamakin su na ganin a yau an wayi gari gas u a kasar Saudiyya ana shiryawa da daukar nauyin taron matan da ke fitowa su na tallata kayan kwalisa a sigar irin tafiyar nan ta kasaitacciyar damisa, wato ‘catwalk.’
Anita Dmycroska cewa ta yi, lallai abin ya burge ta, amma kuma har yanzu ta na al’ajabi.
Tuni dai Yarima Mai Jiran Gado, Muhammad bin Salman, wanda a yanzu shi ne ke rike da mulkin kasar ya fara fatali da wasu dokokin da Saudiyya ta gindaya a baya, inda ta haramta wasu abubuwa da shagulgula.
Cikin wasu da aka haramta a baya, amma a yanzu ya halasta su, sun hada da haramta wa mata tukin mota, shiga silima kallon fina-finai da kuma haramta wa mata shiga sinadiyan kallon kwallon kafa. Duk wadannan yanzu an halasta su a kasar Saudiyya.