Sanatoci sun yi cacar-baki kan ko jihohin Kogi da Anambra na da arzikin danyen mai

0

Majaliasar Dattawa ta umarci Kwamitin Lura da Harkokin Danyen Man Fetur ya binciki rigimar da ake tabkawa dangane da makomar jihohin Kogi da Anambra da aka yi ikirarin ko su na da arzikin danyen man fetur.

An yanke wannan shawara ce bayan wani sanata daga Kogi da na Anambra suka fara sa-in-sa a tsakanin su, bayan da Sanata Chukwuka Utazi daga Anambra ya ja hankalin sauran sanatocin, inda ya ce wani dan jihar Anambra da gwamnati ta nada kwanan nan ya furta cewa jihar ta na da arzikin danyen man ferur.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Mike Emuh, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Al’ummomin da ake Hako Mai A Yankunan su, ya bayyana wa sarakunan gargajiya na jihar cewa gwamnatin tarayya ta amince a kafa kananan matatun mai 10 a cikin yankuna 211 na jihohin da ke da arzikin danyen mai.

Emuh ya ce daya daga cikin karamin matatar man za a kafa shi ne a Anambra.

Har ya kara da cewa kamfanin zai samar da guraben aiki ga mutane 10,000 da tuni gwamnatin tarayya ta amince a gina su.

Ya kuma ce a cikin wadannan mutane dubu 10,000, dubu 1000 a jihar Anambra za a dauke su.

Emuh ya kara yi wa sarakunan jawabin cewa ya zo jihar ne domin ya tambayi sarakunan kowa ya nuna inda inda ya ke so a kafa kamarar matatar a yankin sa.

Sannan kuma su fara tattara sunayen matasan da suke so a dauka aiki.

Sanatocin biyu sun yi ta kawo hujjoji daga cikin abubuwan da suka faru a baya da kuma hukuncin da suka karanto su ka ce gwamnagtin Jonathan ce ta yanke shi a lokacin.

Utazi ya yi tir da wannan sanarwa, inda ya ce ai har yau ba a tabbatar da yakinin ko jihar Anambra na cikin jihohi masu arzikin danyen mai ba.

Ya ce ai a ranar 30 Ga Agusta, 2012 ne gwamnatin Goodluck Jonathan a kan kuskure ta lissafa Anambra a jerin jihohi masu arzikin danyen mai.

Hakan ne ya haifar fa mummunar zanga-zanga a Kogi da Anambra, jihohin da suka mallaki rijiyar mai mai lamba OPL 915, 916 da kuma 917 tare da Anambra.

Tashin Sanata Dino Melaye na jihar Kogi ke da wuya, sai ya ce wadancan sanatocin biyu makaryata ne, karya suka kantara wa Majalisar Dattawa.

Daga nan shi ma ya dauki dogon lokaci ya na bayyana nasa bangaren na hukuncin da gwamnatin Jonathan ta yanke dangane da rikicin rijiyoyin man a wancan lokacin.

A karshe dai majalisa ta mika rikicin a hannun kwamitin kula da harkokin danyen man fetur domin ya yi bincike.

Share.

game da Author