Daukacin Sanatocin Najeriya sun jingine zaman majalisa na yau, domin jimamin ibtila’in da ya fada wa Sanata Dino Melaye, yayin da ya diro daga mota a kan hanyar zuwa kotu, har ya ji ciwo a jiya Talata da rana.
Sanatocin sun isa asibitin yau Labara da misalin karfe 1:29 na rana a cikin manyan motoci kirar bas-bas guda uku, bayan sun katse zaman majalisa na yau Laraba.
A wata sabuwa kuma, Majalisar Dattatawan dai har ila yau ta kuma gayyaci Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Ibrahim Idris, domin ya gurfana a gaban da tangane da jula-jular rikicin Dino Melaye.
Shi ma Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kogi, Ali Janga, ya tabbatar da cewa Dino ya diro daga mota da nufin ya gudu a kan hanyar su ta kai shi Lokoja. Ya ce amma da ya ke a cikin Abuja ne ya diro, ya na wani asibiti mai suna Zankli, a Abuja har zuwa jiya Talata kafin daga bisani a kama shi a maida shi Asibitin Tarayya.
Ana tuhumar Dino ne da laifin yi wa Shugaban Ma’aikatan Jihar Kogi kazafin cewa ya tura wasu makasa domin su kashe Dino, alhalin kuwa daga baya aka gano cewa karya Dino ya kantara masa a gaban ‘yan sanda.
Baya ga wannan kuma, ana binciken sa da zargin taimaka wa wasu makasa da makamai da kudade domin su tada hankula a jihar.
Wadanda aka kama din ne suka shaida wa ‘yan sanda cewa Dino ne ke daukar nauyin su.
Kakakin Dino Melaye ya fitar da takarda mai bayyana cewa Sanatan bai karya doka ba, ana dai yi masa bi-ta-da-kulli ne kawai. Ya ce kuma karya aka yi wa Dino da aka ce ya fito ta taga zai gudu. Ya ce idan ba a manta ba, ai Dino ya shigar da kara a Abuja inda ya nemi a maido shari’ar a Abuja daga Lokoja, inda tuni ya nuna wa Sufeto Janar na ‘yan sanda cewa akwai barazana a rayuwar sa a Lokoja.
A gefe daya kuma sanatan na fuskantar kiranye daga bangaren INEC tun bayan da wasu jama’ar mazabar sa suka shaida wa INEC cewa sun gaji da wakilcin sa, don haka suna son su musanya shi da wani.
A halin yanzu batun yi masa kiranye ya na a gaban Kotun Koli.
Rundunar ‘yan sandan Abuja ta ce sun cafke Dino a asibitin Zankli, kuma za a gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja.
Jami’an tsaro sun ce wasu ‘yan daba ne suka bi motar su da motoci biyu, inda suka yi masu shinge a cikin jerin gwanon motoci, shi kuma Dino ya dira ta taga, suka dauke shi.
A yanzu dai sun ce tunda an sake kama shi, za a kai shi kotu ko ya na so, ko ba ya so.
A lokacin da ake rubuta wannan labari, Sanata Dino Melaye na Babban Asibitin Tarayya da ke Abuja, inda ‘yan sanda ke tsare da shi, sun bayan da suka fito da shi daure da ankwa a kan gadon daukar marasa lafiyar da aka kais hi asibitin Zankli, a jiya Talata da a yamma.
Discussion about this post