Sanatoci sun fara gajiya da batun sauya ranakun zabe

0

Majalisar Dattawa ta yamutsa gemu a kan batun sauya ranakun zabe, inda a karshe dai wadanda suka kusa hakura da sauya ranakun zabe suka yi rinjaye.

Wannan zazzafar mahawara ta faru ne bayan an koma zaman majalisa daga kwatagwangwamar sace Sandar Majalisa da wasu ’yan ta-kife nasu goyon bayan Sanata Omo-Agege suka yi a yau Laraba da safe.

An bai wa Sanatoci da dama fili kowa ya rika tashi ya na bayyana ra’ayin sa game da kudirin sauya ranakun zaben, wanda suka aika wa Shugaba Muhammadu Buhari, amma ya ki amincewa da shi a ranar 13 Ga Maris, 2018, ballantana ya sa masa hannu ya zama doka.

Dama dai Sanata Nazifi Suleiman ne na jam’iyyar APC daga jihar Bauchi shiyyar Arewa ya fara kitsa batun sauya ranakun zaben bayan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta aza ranakun zaben na 2019 a cikin watan Fabrairu da ya gabata.

Sanata Ahmed Lawan, wanda shi ne Shugaban Masu Rinjaye, ya ce ko sau nawa za a maido kudirin, to ba zai amince da shi kamar yadda dama tun farko ya ki amincewa da shi.

“Jama’a ya kamata fa mu lura zabukan da aka gudanar baya, duk babu wanda Majalisar Dattawa da ta Tarayya suka sauya wa INEC ranakun da suka aza za su gudanar da zabe. Don me za mu tsaya mu na ta ja-in-ja akan ranakun zabe alhali ga batutuwan nan birjik wadanda a kan su ne ma aka zabe mu mu tattauna su, sai mu ka karkata a kan ranakun zabe kawai?”

Shi ma Mataimakin Shugaban Majalisa, Ike Ekweramadu, ya ce shima a ta sa fahimtar Shugaba Buhari bai yi wani kuskure ba da ya ki amince wa da batun sauya zaben.

“Ni ina ganin tunda dai a cikin kudirin da muka aika masa, akwai wadanda ya amince da su, to kamata ya yi mu tsame wadanda ya amince da su din, mu maida masa, domin mu wuce wannan wurin, wurin da bai amince ba kuwa, sai mu bar wa Kwamitin Harkokin Zabe su je su sake dubawa.”

Kokarin da Dino Melaye ya yi domin a jingine batun zuwa wani lokaci a sake karanta shi a karo na biyu a majalisa, bai yi nasara ba, domin akasarin majalisar ba ta goyi baya ba.

Dino cewa ya yi, “ni ina ganin a jingine batun mu je mu kara yin bincike, domin kada a koyaushe a rika bar wa INEC wani karfin iko har wanda ba ta cancanta ba.”

Shi kan sa Ikweremadu bai amince da wannan shawarar ta Dino ba, kamar yadda sauran ma ba su amince da ita ba.

“Ina ganin mu bar Kwamitin Majalisa kan Harkokin Zabe su je su sake duba bangaren da Shugaba Buhari bai amince da shi ba, sauran bangaren da ya amince da shi kuma, sai mu ci gaba da dubawa a nan majalisa tukunna, zuwa lokacin da za a maida masa gaba daya domin ya rattaba hannu a kai.”

A karshe dai duk aka amince da shawarar da Ikweremadu ya bayar.

Share.

game da Author