A ranar Laraba ne Sanatocin Najeriya suka jingine zaman Majalisar Dattawa, inda suka rankaya Babban Asibitin Tarayya na Abuja domin zuwa su jajanta wa Sanata Dino Melaye, wanda aka kwantar asibiti, bayan ciwon da ya ji sanadiyyar dirowa daga cikin motar ‘yan sanda, a lokacin da suke kan hanyar zuwa Lokoja inda za a gurfanar da shi kotu.
Sai dai kuma jami’an ‘yan sanda sun hana tawagar sanatocin gaba dayan su shiga cikin dakin jiyyar da aka kwantar da Dino, suka ce sai dai Shugaban Majaliasa, Mataimakin sa da kuma wasu mambobin majalisar biyu ne kadai za su iya shiga.
Bayan sun fito, Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa Dino na samun sauki sosai. Sai dai ya nuna damuwa a kan yadda kusan kwana daya Sanatan ya na kwance, amma bai ci abinci ba.
Majibinta asibitin, wanda shi ne babban asibitin gwamnatin tarayya a Najeriya, sun shaida wa Saraki cewa, ba hakkin su ba ne bai wa majiyyaci abinci. Kula da lafiyar sa da magungunan sa ce hakkin su.
Su ma jami’an ‘yan sanda da aka yi musu wannan korafin, sun ce ba za su yi kasadar bai wa sanatan abinci ba, domin gudun abin da ka iya zuwa ya dawo. Suna gudun kada ya ci wani abu bayan abincin da suka ba shi, daga baya kuma cibi ya zama kari.
Idan za a iya tunawa, a cikin wani bidiyo da aka nuno Dino zaune a kan kwalta bayan ya diro daga cikin motar ‘yan sanda, ya rika yi wa jami’an tsaron barazanar cewa zai fa kashe kan sa don kawai ya goga musu sharrin da za su afka cikin tsomomuwa.
PREMIUM TIMES ta gano cewa su kuma iyalan Dino Melaye da aka nemi su rika kawo masa abinci, sun bayyana cewa ba za su ba shi abinci ba, har sai jami’an ‘yan sanda sun sanar da su cewa maigidan su Dino Melaye ya na hannun su.
Shi kuwa Sanata Shehu Sani, ya bayyana a shafin sa na Facebook, cewa magana ta gaskiya ba zai iya cewa Dino Melaye na murmurewa ba.
Ya ce mutumin da kyar ma ya ke iya bude baki ya yi magana, kuma an sa masa bandeji a wuyan sa, ta ya zai ce ya na murmurewa?
“Duk da dai a lokacin da mu ka je ba daure ya ke da ankwa ba, tunda ni ba likita ko nas ba ne, ba zan iya hakkakewa da sauki ko rashin sauki a jikin sa ba.”
Wani likita da ke aiki a asibitin Zankli ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa a lokacin da aka fara kai shi can, akwai alamun kamar sanatan karya kashin bayan sa. Amma dai ba a hajaran-majaran ya ke ba.
Sanatocin da suka je dubiya, sun kuma nuna damuwar su da irin yadda aka jibge kitika-kitikan ‘yan sanda su na kewaye dakin jiyyar, kuma su na korar masu matsawa kusa da niyyar shiga su duba Dino.
Dino dai yana nan a kwance a asibiti makalkale da ankwa, sannan kuma Hukumar zabe zata fara tantance rattaba hannayen da ‘yan mazabarsa suka yi na yi masa kiranye.