Sanata Bukar Mustapha ya rasu

0

Allah yayi wa sanata Bukar Mustapha, dake wakiltar Katsina ta Arewa rasuwa.

Marigayi Bukar Mustapha ya rasu ne bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya da yayi fama da ita.

A makon da ya gabata ne akayi jana’izan shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Buba Jibrin. Shima ya rasu ne bayan gajeruwar rashin Lafiya da ya yi fama da ita.

Kamar yadda Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito, dan’uwan mamacin, Kanta Bukar ne ya sanar da haka.

Share.

game da Author