Sabuwar kutunguilar gwamnonin APC na neman jefa jam’iyyar cikin sarkakiya

0

A wani sabon yunkurin da gwamnonin APC ke yi domin su tirsasa gudanar da zaben shugabannin jam’iyya, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da shawara a yi, wasu gwamnonin APC sun bazama shirya kutunguila da kisisinar murde tsarin da jam’iyya ta gindaya, ta hanyar kokarin su na rubuta wasika amma da niyyar sa wata rana can da ta rigaya ta gabata, a matsayin sun dade da rubuta wasikar.

Wannan ya sa gwamnonin sun tilasta wa Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Mala Buni da ya gaggauta rubuta takardar kiran taro ga Babbban Kwamitin Jam’iyya, ya kira taro a ranar Litinin 9 Ga Afrilu.

A taron su na ranar Laraba, gwamnonin sun roki jami’an APC da kowa ya amince da shawarar da Buhari ya bayar na soke karin wa’adin, sannan kuma a sake zabe. A lokacin ko wani kwamiti da aka kafa bai ma kai ga mika rahoton aikin da aka dora masa ba.

Kwamitin wanda ke karkashin Gwamna Simon Lagong na Filato, ciki har da Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Sai dai kuma wasu mambobin jam’iyyar sun ja kunnen daukar duk wani matakin da zai iya kauce wa wani batu da tuni ya ke a gaban Babban Kwamitin Zartaswa na jam’iyya, tunda jam’iyyar ce ta bayyana haka a karkashin doka ta 18 ta jam’iyyar.

Gwamnonin da ke wannan kulle-kullen su na so ne su yi wa kwamitin Lalong riga-malam-masallaci ne, ta hanyar saboda ba su so kwamitin ya bada rahoyon da zai sa a dauki wani mataki, a lokacin da Shugaban Kasa ba ya Najeriya. Dalili ke nan su ke so a yi taron gangami na uwar jam’iyya tun kafin Buhari ya tafi Landan halartar taro da kuma ganin likita.

Amma kuma an fahimci cewa gwamnonin sun damu kwarai kan yadda wani sashe na dokar APC da ke nuni da yadda za a kira taron na Manyan Kwamiti na jam’iyyar.

Dokar APC ta Sashe na 25B(II), ya ce “Babban Kwamitin Uwar Jam’iyya zai kira taro ne sai idan akalla an rage saura kwanaki bakwai kafin ranar zabe.”

To ganin cewa ba za su iya samun sarari na kwanaki 7 da doka ta tanadar ba, wato tsakanin Laraba zuwa Litinin, sai gwamnonin APC suka nemi Sakataren Jam’iyya da ya rubuta takardar gayyata taro, amma ya rubuta wata rana can ta baya da ta shude, ba ranar da za a rubuta wasikar ba. Wato zai rubuta ranar 3 Ga Afrilu, ba 4 Ga Afrilu ba, wadda ita ce aka rubuta wasikar a zahiri.

Sun yi haka ne da nufin su ribbaci jama’a, su nuna musu cewa an rigaya an tura wasikar gayyata tun a ranar Talata, amma a hakikanin gaskiya, har 8: na dare a ranar Labara ba a ma sa wa wasikar hannu ba.

Amma shi kuma Mala Buni, sai ya ki bin umarnin gwamnonin, ya ki aikawa da wasikar gayyatar. Ya ce idan ya yi haka, to zai iya shiga cikin matsala, matsawar aka gano cewa ya na cikin wannan kumbiya-kumbiyar.

“Shi sakataren jam’iyyar ai ya sani sarai cewa ko a cikin gwamnonin sai an samu wani magulmacin da zai tona masa asiri.” Haka wani dan jam’iyyar APC wanda ya san dukkan irin wainar da ake toyawa ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Ya zuwa ranar Alhamis, 9:07 na safe, wani sanata wanda ke cikin Babban Kwamitin Zartaswar APC, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa har zuwa lokacin bai karbi tasa wasikar gayyata zuwa taron ba da suka kulla cewa za a gudanar a ranar Litinin mai zuwa.

Sanatan ya ce ya samu labarin cewa an yi shirin za a aika wa kowa ta sakon tes a wayoyin kowa, amma dai har zuwa lokacin bai ji sakon ya shiga wayar sa ba.

Sanata Yerima daga Zamfara, da kuma Hon. Ado Doguwa daga Kano, dukkan su mambobin ne, amma an kira lambobin su, ba su dauka ba. Sannan kuma an tura musu sakon tes domin a ji ko sun karbi sakon takardar gayyata ko da ta hanyar sakon tes na waya, nan ma ba su bayar da amsa ba.

GAGGAWAR WANKA DA RUWAN KWATAMI

Wata majiya ta tabbatar da cewa matsawar da aka yi amfani da wannan makarkashiyar, to jam’iyyar APC za ta tabka babban laifi. Kuma za ta kauce wa tsarin da dokar kasa ta gindaya.

Da dama a cikin jam’iyyar na fargabar cewa Mala Buni a karshe dai zai iya amincewa ya yi abin da gwamnonin ke bukata.

“Ba za mu amince da wannan asarkala ta faru a jam’iyyar mu ba, saboda shugabannin da ke cewa ba za su taba yarda su aikata abin da ba daidai a cikin jam’iyyar ba, an wayi gari a yau kuma su ne ke ta kokarin tafka haramtattace kuma danyen hukuncin da zai kai mu ga da-na-sani, saboda wata biyan bukatar son zuciyar su kawai.” Haka wani dan jam’iyyar ya shaida wa PREMIUM TIMES a fusace, amma kuma ya nemi a sakaya sunan sa.

Sai dai kuma kakakin yada labaran jam’iyyar APC, Bolaji Abdullahi, ya ce bai san da wannan batu na rubuta wasika a saka ranar da ta rigaya ta gabata ba.

Ya ci gaba da cewa da shi aka fara taro a ranar Laraba, kuma da shi aka tashi, amma bai ji ba, kuma bai san da wani labari na kokarin da wasu gwamnoni ke yi ko suka yi domin su tirsasa Sakataren APC, Mala ya rubuta wata wasika ba. Haka Abdullahi ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Share.

game da Author