Sakataren Kula da Sufuri da Zirga-zirga na Hukumar Babban Birnin Tarayya, Abuja, ya fito da wasu sabbin ka’idojin tukin motocin haya masu daukar fasinja a Abuja.
Kayode Opeifa, ya ce ma’aikatar Sa ta fito da ka’idojin ranar Litinin bayan wani taro da ta yi da direbobin tasi.
Ka’ida ta farko ita ce, dukkan manyan motocin haya, bas-bas, tasi, Keke-NAPEP da baburan acaba masu haya a garuruwan kewayen Abuja ko cikin Abuja, to tilas su kasance dauke da jar lambar mota, maimakon ruwan bula wacce sun san ba ita ce lambar motocin haya ba.
“Sannan kuma duk wata motar haya da ake haya da ita a Abuja, to ya kasance ta na dauke ne da lambar Abuja, daga I Ga Oktoba, 2018.
“Duk tasi da za a yi haya da ita a Abuja, to ya kasance ta na da na’urar sanyaya jiki da mota, wato air condition kafin nan da ranar 1 Ga Oktoba, 2018.
“Duk motocin haya da ke Abuja su kasance su na dauke da takardun shaidar cancantar ingancin amincewa a yi haya da su. Za su mallaki kwafi biyu na wannan takardar shaida daga ofishin bada iznin cancantar da ke Abuja.
Opeifa ya kara da cewa kowane direban motar haya ya kasance ya na da gangariyar lasisin tuki, wanda bayan ya mallake shi, sai ya je sakateriyar Hukumar FCT sun sake tabbatar da sahihancin sa.
Ya kara da cewa kowane direban motar haya tilas ya rika mallakar takardar biyan haraji a Abuja.
An kuma yarda duk wanda ya cika wadannan sharudda ya rika dauka da ajiye fasinja a Abuja, matsawar dai inda aka amince masa ya tsaya ya ajiye ne, ko kuma wurin da doka ta ce ya tsaya ya dauki fasinja.
Laifi ne babba direban motar haya a tsaya inda zai takura wa motoci masu wucewa ko masu gilmawa.
Direbobin Keke-NAPEP su tabbatar da sun rika bi hanyoyin da doka ta ce su rika bi kawai.
Masu Keke-NAPEP da masu baburan acaba ba a yarda su yi haya da ababen hawan da Hukumar Abuja ba ta ba su tambarin shaidar iznin aiki a Abuja da kewaye ba.
Dukkanin masu manyan motocin haya, bas-bas, taksi, Keke-NAPEP, su garzaya ofishin da za a yi musu rajistar kididdigewa a bayar da iznin haya a Babban Birnin Tarayya da kewaye.
An dakatar da bada lasisin iznin yin haya a Abuja, har sai yadda hali ya yi.
Daga yau an hana kungiyoyin direbobin haya da manyan motoci, taksi, Keke-NAPEP da baburan acaba su yi wa wani rajistar zama mamba a cikin su.
Sakateriyar Hukumar Babban Birnin Tarayya na bukatar dukkan masu kamfanonin motocin haya da ke aiki a karkashin kafanoni su kai jerin yawa da lambobin adadin motocin da ke haya a karkashin kamfanonin su, kafin nan da ranar 13 Ga Afrilu, 2018.
Discussion about this post