RIGAKAFI: Gwamnatin Kaduna za ta biya dakatai naira 10,000 duk wata

0

Kwamishinan kula da kananan hukumomi da sarakunan gargajiya na jihar Kaduna Kabiru Mato ya bayyana cewa daga yanzu gwamnatin jihar za ta dunga biyan masu unguwani da dakatan kauyuka su 17,139 dake fadin jihar Naira 10,000 duk wata don su taimakawa gwamnati wajen horon mutanen garuruwan su da su mara wa shirin yin rigakafin cututtuka da gwamnatin jihar ke yi baya.

Ya sanar da haka ne ranar Laraba a taron manema labarai a garin Kaduna inda ya kara da cewa yin haka ya zama dole domin karfafa yi wa yara alluran rigakafi musamman a yankunan karkara saboda a basu kariya daga kamuwa da hana yaduwar cututtuka.

” Samun goyan bayan masu unguwani da dakatai zai taimaka wajen karfafa yin allurar rigakafin cutar shan inna da sauran cututtuka a yankunan karkara dake fadin jihar.

Kwamishina Mato ya ce shi kan sa gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya tabbata an yi wa ya’yan sa wannan allura domin ya zama abin koyi ga sauran iyaye.

Share.

game da Author