PREMIUM TIMES Hausa ta kawo muku jerin Sanatoci da Mambobin Majalisar Tarayya su 9 da suka rasu a lokacin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari. Sanatoci 4 da Mambobin Majalisar Tarayya 5 ne suka mutu a lokacin mulki Buhari, daga 2015 zuwa Afrilu, 2018.
Wani bincike ya nuna cewa akasarin mamatan duk sun bar duniya ne bayan sun haura shekaru 50 a duniya. Sai dai uku daga cikin su ne kawai suka haura shekaru 60.
Sannan kuma babu wanda ya rasu sanadiyyar hadari, rikici ko ibtila’i na wani bala’i. Daga gajeruwar rashin lafiya sai matsananciyar rashin lafiya da wasu ake dangantawa da bugawar zuciya.
1 – Sanata Mustapha Bukar daga Shiyyar Katsina ta Arewa, wanda ke wakiltar mazabar Daura, ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, shi ne na baya bayan nan da ya rasu a makon da ya gabata. Ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya.
2 – Sanata Ahmed Zanna, daga Jihar Barno, ya rasu tun ma kafin a kaddamar da sanatocin. Ya rasu ana saura wata daya a kaddamar da su. An taba danganta shi da Boko Haram a cikin 2012, a zangon sa na farkon zama Sanata, lokacin da aka kama wani gogarman Boko Haram mai suna Shu’aibu Mohammed Bama a gidan sa na Maiduguri.
3 – Hon. Buba Jibrin, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Lokoja, daga jihar Kogi. Ya rasu ya na da shekaru 58, kuma ya taba zama kakakin majalisar jihar Kogi. Shi ne a wajen makokin sa Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dagara ya yi jawabi mai ratsa jiki, inda ya ce “Ita dai mutuwa kaddara ce da kuma lokaci daga Ubangiji. Amma ba dadin mu ba ne yadda mu ke yawan jana’izar mambobin mu. Mu na addu’ar Allah ya yi mana tsawon rai. Amma ban taba tunanin hakan zai faru ba, inda cikin kankanin lokaci za mu yi jana’idar Sanatoci 3 da mambobi 5.”
4 – Sanata Isiaka Adeleke daga Jihar Osun, ya rasu ya na da shekaru 62 a cikin Afrilu, 2017 sakamakon bugun zuciya. Adeleke ya taba yin gwamna. Sau uku ya na yin sanata. Sai dai kuma an yi ta zargi da yada ji-ta-ji-tar cewa asiri ne aka yi masa ko kuma guba aka zuba amasa a abinci. Kanin sa Ademola Adeleke ne ya zama sanata bayan mutuwar sa. Ademola shi ne sanatan nan da ya ci zabe a karkashin PDP bayan zaben cike gurbin da marigayi Isiaka ya bari. Shi ne kuma sanatan nan da a yanzu ba ya jin kunyar tikar rawa ko a gaban surukar sa.
5 – Sanata Ali Wakili daga jihar Bauchi ya rasu a ranar 16 Ga Maris, 2018, a Abuja. Kuma a Abuja din aka rufe gawar sa. An bada rahoton cewa ciwon bugun zuciya ne ajalin sa, domin kwana daya kafin rasuwar sa, da shi aka daura auren ‘yar gidan Aloko Dangote a fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II. Ya na da shekaru 58 ya rasu. An ce yanke jiki ya yi a gidan sa da ke Gwarimpa ya fadi. Tsohon babban jami’in kwastan ne, bayan ya yi ritaya ya shiga siyasa.
6 – Hon. Elijah Adewale, Dan Majalisa mai wakiltar Ifako/Ijaiye daga jihar Lagos. Ya yanke jiki ya fadi ya mutu a gidan sa, da jijjifin safiyar Alhamis, 21 Ga Yuli, 2016 a gidan sa da ke Abuja. Ya rasu ya na da shekaru 65. Shi ma kwana daya kafin rasuwar sa, an tabbatar da cewa ya halarci wasu kwarya-kwarya taron ganawa da wasu daidaikun mambobin majalisa.
7 – Hon. Bello Sani, shi ma dan jam’iyyar APC ne, ya rasu ranar 15 Fabrairu, 2017 a lokacin ya na da shekara 51 da haihuwa. Daya daga cikin hadiman sa ya bayyana cewa Bello ya dade ya na fama da jiyya kafin rasuwar sa. Shi ne wanda ya wakilci Kananan Hukumomin Mashi da Dutsi daga jihar Katsina.
Hon. Abdullahi Wammako, dan Majalisar Tarayya ne daga jihar Sokoto. Ya rasu a wani asibiti da ke Abuja a ranar 14 Ga Yuli, 2017, bayan wata gajeruwar rashin lafiya. Shi ke wakiltar kananan hukumomin Kware da Wamakko. Shi ma dan jam’iyyar APC ne, kuma wannan ne zangon sa na farko kafin rasuwar sa. Ya rasu ya na da shekaru 50 da haihuwa.
Hon. Musa Baba ya wakilci kananan hukumomin Nasarawa da Toto na jihar Nasarawa a karkashin APC. Ya rasu ranar 17 Ga Maris, 2016 ya na da shekaru 50 a duniya. Ba a bayyana musabbabin rasuwar ta sa ba. Ya yi zangon sa na farko daga 2011 zuwa 2015. Ya rasu ne a cikin zangon sa na biyu.