A ranar Alhamis ne babban sakataren hukumar inshorar kiwon lafiya ta kasa NHIS Yusuf Usman ya karyata zargin da ake yi masa na yin amfani da kudin hukumar da ya kai naira biliyan 25 wajen siyan hannayen jari wa hukumar.
Yusuf ya bayyana cewa bai taba kudin hukumar ba ballantana har ya siyawa hukumar hannayen jari duk da cewa dokar hukumar ta amince masa yayi hakan.
Wannan amsa ne ga korafin da jaridar THISDAY ta buga cewa wai ya siya wa hukumar NHIS din hannayen jari.
A taron manema labarai da yayi a ofishin hukumar, Yusuf ya yi amfani da wannan dama ya roki gafara ga wadanda ya saba wa lokacin da suka yi ta samun rashin jituwa da ministan lafiya, Isaac Adewole da yayi sanadiyyar dakatar dashi da akayi.
A karshe shugaban hukumar gudanarwa na NHIS Enyantu Ifenne ta yi kira ga duk ma’aikatan hukumar da a yafe wa juna kuma a hada hannu gaba daya don ci gaban hukumar da kiwon lafiyar mutanen kasa gaba daya.