Najeriya za ta ci gaba da samun tallafi daga GAVI – Minista Adewole

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa Najeriya ta sami karin shekaru 10 don ta ci gaba da samun tallafin samar da magungunan allurar rigakafi wanda kamfanin GAVI ke bata.

Adewole ya sanar da haka ne a taron samun madafa kan awar da cutar shawara wanda kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta shirya a Abuja.

Idan ba a manta ba a shekarar 2014 ne ministan kudi Ngozi Okonjo-iwela ta bayyana cewa Najeriya ta fita daga jerin kasashen dake fama da matsalar karancin kudi wanda haka ya sa kamfanin GAVI ta yanke shawaran cire Najeriya daga cikin kasashen da take tallafawa wurin samar da magungunan rigakafi.

Amma sai dai wani gudun ba hanzari ba, Adewole ya ce hakan ba zai yiwu ba domin Najeriya bata dade daga fita daga cikin matsalar koma bayan tattalin arziki ba wanda haka ya sa kasar ta roki alfarmar Kamfanin GAVI da ta bata shekaru 10 domin ta sami damar kafa matakan da za su taimaka wajen bunkasa fannin kiwon lafiyar ta domin iya tafiyar da shirin yin alluran rigakafi batare da jiran tallafin kanfanin ba.

Daga karshe shugaban WHO Tedros Ghebreyessus ya ce kungiyar su za ta ci gaba da mara wa Najeriya baya don ganin ta cin ma burin ta.

” Za mu iya samun nasara ne idan mun yawaita masana’antun sarrafa magungunan allurar rigakafi musamman a kasashen Afrika domin kawar da matsalar tsadan magungunan da kasashen Afrika ke fama da su.”

Share.

game da Author