Limamin wani coci dake jihar Legas mai suna Joshua Ibeneme ya roki kotu ta raba auren sa da matar sa mai suna Uzoamaka saboda zargin ta da aikata lalata da wasu maza dake aiki a cocin.
Ibeneme ya ce ya fara zargin matar sa ne da aikata lalata a lokacin da wasu limamen cocin biyu suka fadi cewa sun kwana da ita da kan su.
Ya kuma ce matar sa ta kaurace masa har na tsawon shekaru biyar sannan ta sa ‘ya’yan su uku da suka haihu tare ba sa ganin girman sa.
Ita kuwa Uzoamaka ta bayyana cewa ta na son mijin ta domin bata da ra’ayin rabuwa da shi.
Ta kuma ce karya mijinta yake mata na aikata lalata da wadannan maza domin wadannan maza sun fadi haka ne don su bata mata suna.
” Na kaurace wa mijina saboda tun faro na yi aure ne don na haihu kawai.”
A karshe alkalin kotun Akin Akinniyi ya hore su da su je su zauna lafiya sannan ya daga cigaba da saurarenkaran zuwa 10 ga watan Mayu.
Discussion about this post