Hukumar bada agajin gaggawa (NEMA) ta bayyana cewa sakamakon binciken da kwamitin da hukumar ta kafa kan hare-haren da aka kai jihar Zamfara, mutane an samu tabbacin mutuwan mutane 54, 71 kuma sun sami raunuka dabam-dabam sannan 7000 kuma sun koma ‘yan gudun hijra.
An kona gidaje sama da 30 sannan an sace shanu 1000 a kauyukan Baudi, Tungan Turkish, Doka, Zanoka, Akuzo da Dogon Ruwa.
” A yanzu haka masu gudun hijira suna zaune ne a kauyukan Hayin dan Bawa, Anka da garin Gusau.” Inji Mohammaed Ibrahim, Jami’in hukumar NEMA.