Shugaban jami’an tsaron na sa kai ‘Civilian- JTF’ Muhammed Babagoni ya bayyana cewa mutanen da suka rasa rayukan su a harin da wasu ‘yan kunan bakin wake mata biyu suka kai a Maiduguri yayi ajalin wani magidanci da wani daga cikin jami’an tsaron sa kai din.
‘Yan kunar bakin wake sun far wa garin Maiduguri da mota shake da bama-bamai inda suka afka wani ginin.
Shugaban rundunar Operation Lafiya Dole’ Nicholas Rogers ya ce sun fatattaki Boko Haram bayan an dauki awowi ana batakashi da ‘yan kungiyar
Ya ce sun sami wannan nasara ne tare da hadin guiwar jami’an tsaro na sa kai ‘civil Defence’,Civilian – JTF, ‘yan sanda da sojin saman Najeriya.
Rogers ya yi kira ga mazauna wannan unguwa da su dawo gidajen su su ci gaba da harkokin su.
” Ina kira da mazauna wannan unguwa da su dawo su ci gaba da harkokin su sannan ina rokon su da su tona duk wani bakon fuska da su ka gani a unguwar.
Ya ce dakarun su sun fantsama daji don bin sahun wadannan miyagun mutane.
Discussion about this post