” Mun gwammace mu haihu ta hanyar gargajiya da mu je asibiti” – Mata a Abuja

0

Wata mazauniyar kauyen Igu dake karamar hukumar Bwari mai suna Asabe Joshua ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa rashin samun ingantaciyyar kiwon lafiya da suke bukata ne ya sa kusan dukkan su sun gwammace su ziyarci unguwar zoma na gargajiyya a kauyen duk lokacin da dayan su ta tashi haihuwa.

Asabe ta ce tsadar magani da rashin basu kula a cibiyar kiwon lafiya dake kauyen ne ya sa dukkan su suka guje wa wannan asibiti.

” A duk lokacin da mace ta je haihuwa a wannan asibiti dole ne sai ta biya Naira 5,000 ko tana da shi ko babu sannan ba lallai bane su kula da ita yadda ya kamata duk da cewa ta biya wadannan makudan kudade.

Allah ya hada mu da wata mata, Binta Nuhu da muke kira Mama, ita har gida zata biyo ka, ta tabbata ka haihu lafiya
sannan ta kula da mace har sai ta warware kuma wani abin kwanciyar hankali a kai shine ba za ka kashe fiye da naira 1000 daya zuwa biyu ba.

Asabe ta ce su kan ziyarci wannan asibitin ne idan lokacin yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafi ya yi ko kuma awo kawai.

Bayan haka gidan jaridar ta yi hira da unguwar zoma, Binta Nuhu inda ta bayyana cewa ta fara wannan aiki ne tun tana shekara 30 sannan ta yi shekara 25 tana wannan aiki.

Ta ce ta koyi wannan aiki ne a cibiyar kiwon lafiyar dake kauyen Kafi Koro a jihar Neja kuma ta karbi haihuwar yara sama da 400 sannan ba mace ko jaririn da taba mutuwa a hannun ta.

Binta ta ce takan bada magugunan cutattar zazzabin cizon sauro da kuma yi wa musu allura idan ta kama.

” Da na kalli fuskar mara lafiya na kan san irin cutar dake damun sa. Na kan siya magungunar da nake ba masu haihuwa ne daga shagunan saida magani dake kusa da su.

A tsokacin da ma’aikaciyyar kiwon lafiyar asibitin dake kauyen Igu Eunice Gajere ta ce mata kan je wajen ‘Mama’ ne saboda rashin kayayyakin aikin da suke fama da shi sannan haka a ake fama da irin wannan matsalar a cibiyoyin da ke makwabtaka da su.

” Ginin asibitin mu ya fara rushewa, babau wutan lantarki da sauran irin abubuwan da asibiti ke bukata.”

‘‘Matan ka zo wajen mu yin awo da yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafi ne kawai, da zaran haihuwa ya zo sai su tafi wajen Mama domin haihuwa.

A karshe shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na kasa (NPHCDA) Faisal Shuaib ya ce hukumar sa na kokarin ganin ta kau da irin wannan matsala da ake fama dasu a wasu sassan kasar nan. Sannan ya kara da cewa za a horas da kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya domin tura su cibiyoyin kiwon lafiya da ke karkara a fadin kasar nan.

Share.

game da Author