Wata mata mai suna Maryam Adegoke ta nemi kotun dake Idi-Ogungun a Agodi jihar Oyo da ta warware auren ta da mijinta mai suna Lukman Adegoke cewa wai sai da ya asirce ta kafin ya aure ta.
Maryam ta ce Lukman ya yi mata sihirin mallakane tu a shekarar 2000 bayan ta kai masa ziyara gidan sa.
” Tun da na shiga gidan sa na kasa gane kai na shekaru uku kenan muna tare. Haka kuma lokacin da na koma gidan iyaye na kwana biyu kawai na iya yi naji bazan iya zama ba, kawai na tattara nawa-inawa na dawo gidan sa.”
Maryam ta ce ko da yake ta haifi ‘ya’ya shida da Lukuman amma tun da idon ta ya waye bata kaunar ta ci gaba da zama da shi.
” Cikin ‘ya’ya shida da muka haifa biyu ne kadai ke a raye wanda daya na hannu na sannan na biyun na hannun Lukman.”
Alkalin kotun Mukaila Balogun ta yanke hukuncin raba auren sannan ta karbe dan dake zama da Lukuman ta ba Mariam.
Alkalin ta ce ta yi haka ne saboda kin zuwa kotu da Lukuman ya yi sannan ta umurci rajistaran kotun ya aikawa Lukuman hukuncin da ta yanke.