A wani karfin hali, Kwamitin Majalisar Tarayya ya yanke shawarar ya gayyaci Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo domin ya bayyana a gaban sa.
Yanke wannan shawara da kwamitin ya yi, ta biyo bayan wani bincike da kwamitin ke yi wa wata hukuma, wadda Osinbajo ne shugaban hukumar gudanarwar wannan hukumar.
Kwamitin dai ya na binciken zargin karya ka’idojin aiki da kwangiloli da ake zargin an tafka a Hukumar Kula da Agajin Gaggawa, NEMA, abin da har ya kai ga dakatar da daraktocin hukumar shida.
Osinbajo shi ne shugaban hukumar gudanarwar NEMA, kuma ‘yan majalisar tarayya na bukatar ya bayyana domin ya yi bayanin rawar da ya taka wajen dakatar da wasu jami’an hukumar da kuma harkallar da ta dabaibaye hukumar baki daya.
Haka kuma wannan kwamiti mai mambobi 35, da ke karkashin Hon. Ali Isa, ya gayyaci Shugaban Riko na EFCC, Ibrahim Magu da wasu jami’ai daga SSS da hukumar fansho ta kasa da kuma ministocin harkar noma da na tsare-tsare da kuma ministar kudi.
Ana zargin NEMA da kuma shugaban ta, Mustapha Maihaja da laifin bayar da kwangilolin sayen shinkafar da za a raba a sansanonin masu gudun hijira har ta naira bilyan 3.1. Sai dai kuma bincike ya tabbatar da cewa kamfanonin da a ka ba kwangilar sayo shinkafar ba su cancanta ba.
Discussion about this post