Matashi ya rataye kan sa a jihar Gombe

0

Wani abin tashin hankali ya auku a kauyen Sarakiyo dake karamar hukumar Akko jihar Gombe shine inda wani matashi dan shekara 13 ya rataye kansah a a cikin dakin sa.

Wannan abin tashin hankalin ya faru ne ranar Litini a gidan wani dan sanda mai suna Abdu Manu dake aiki a ofishin ‘yan sandan dake Gwana a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Mary Malum da ta sanar da haka ta furta cewa rundunar ta sami labarin wannan mummunar abu ne a lokacin da shi mahaifin yaron ya taho ofishin ‘yan sandan domin ya shaida musu abin da ya faru.

Kamar yadda ya fadi, mahaifin yaro ya bayyana cewa, mahaifiyar yaron ne ta gaya masa abin da ya faru cewa tunda ya dawo daga makarantar Islamiyya ya shige daki, to fa sai gawar sa.

Yanzu dai an kai gawar yaron asibiti, sannan ‘yan sanda za su ci gaba da yin bincike akai.

Share.

game da Author