Matasan Najeriya sangartattun jahilai ne – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya soki matasan Najeriya, wadanda ya kira sangartattu, saboda dabi’ar su ta jiran tsammanin samun abu ba tare da sun tashi sun ci gumin kan su ba.

“Sama da kashi 60 cikin 100 na yawan al’ummar Najeriya duk matasa ne ‘yan kasa da shekaru 30, kuma da yawan su ba su je makaranta sun nemi ilmi ba, kawai su na ikirarin cewa Najeriya kasa ce mai arzikin man fetur. Saboda haka, sai su zauna a sangarce su na jiran su samu gidajen zama, kula da lafiya da kuma ilmi duk a kyauta.”

Haka jaridar The Cable ta ruwaito shi ya na furtawa a lokacin da ya ke jawabi ga taron Shugabannin Duniya a Taron Tattauna Kasuwanci da Tattalin Arziki a Landan, ranar Laraba.

Dama kuma cikin watan Fabrairu, 2016, Buhari a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Telegraph, ya ce wasu ‘yan Najeriya mazauna Ingila, musamman matasa, duk sun karkata ne wajen aikata munanan laifuka don haka bai cancanta Ingila ta rika ba su mafaka su zauna ba.

Daga jiya zuwa yanzu dai gaba daya kasar nan, duk jama’a sun karkata ne wajen jinjina wannan furuci na Buhari, wanda da dama ke cewa bai kamata ma, kuma kasassaba ce shugaba ya fita waje ya na aibata kasar sa.
A farkon wannan shekara ne wani bincike da sharhi da Jami’ar Rice ta gudanar a Amerika, ya tabbatar da cewa ‘yan Najeriya bakin da suka fi dukkan sauran baki daga kowace kasa ilmi.

Bidiyon furucin da Buhari ya yi a Landan ya na ta yawo a soshiyal midiya, inda matasa a fadin kasar nan, musamman a Arewa ake ta yin tir da kalamin.

Share.

game da Author