Mata ta kwarara wa mijin ta tafasasshen ruwa da ta garwaya da barkonu

0

Wani abin takaici ya faru a Minna jihar Neja shine wata matan aure mai suna Janet Mohammed ta kwara wa mijinta Alaska Mohammed tafasashen ruwa hade da barkonu a jiki.

Wannan tashin hankali ya auku ne bayan ma’auratan sun sami sabani a tsakanin su.

” Mohammed ya bayyana cewa sabanin ta auku ne saboda kin amincewa wa matarsa Janet ta kai dan su dan watanni 11 coci sannan da nuna halin ko in kula game da rashin lafiyar dan da take yi.”

” Ya ce bayan da mahaifiyar shi ta shiga tsakanin su ta samu ta sasanta su ashe mai dakinsa ba ta hakura tana kafe da shi a ziciyar ta. Domin ta rantse ba shima sai yaje radadin dukan da yayi mata.

” A daidai ina cin abincin safe wato karin kumallo, sai matata ta silalo dafaf-dafaf rike a hannunta ashe tafasasshen ruwan zafi ne da da tafasa shi da barkonu irin mai zafin nan. Ni ko ina ta fama da abinci ina kallon talabijin a falo sai ko ta sheka min wannan ruwa. Kafin in ankara ta falla da gudu ta fita gidan.

Wannan ruwa sai da ya daye min fatar jiki da fuska ta.”

Mohammed ya ce ya sanar wa ‘yan sanda wanan mummunar aiki da matar sa ta aikata. Kakakin rundunar ‘yan sanda ya tabbatar wa manema labarai aukuwar wannan abu sannan ya ce suna nan suna gudanar da bincike akai.

Share.

game da Author