Jami’in hukumar kula da aiyukan masu yi wa kasa hidima (NYSC) reshen jihar Kano Ladan Baba ya bayyana cewa cikin wadanda suka karanci aiyukkan kiwon lafiya da suke yi wa kasa hidima a jihar za su su tallafa wa mazauna karkara 8,000 da gwaje-gwajen cututtuka, basu magani, da shawarwari domin inganta kiwon lafiyar su.
Ya sanar da haka ne a taron kula da kiwon lafiyar mutane da aka yi a kauyen Rugar Duka dake karamar hukumar Kura.
Baba ya kara da cewa masu yi wa kasa hidima sun yi haka ne domin tallafa wa mazaunan karkara musamman talakawa a cikin su da ingantaciyar kiwon lafiya.
” Masu yi wa kasa hidima za su tallafawa mutane 2,000 a kauyuka hudu da suka zaba daga wannan karamar hukumar sannan sun kuma taimaka wajen wayar da kan mazauna kauyukan kan mahimmancin samun ilimin boko, kiwon lafiya da tsaftace muhalli.”
A karshe uwargidan gwamnan jihar Kano Hafsat Ganduje ta jinjina wa aiyukkan inganta kiwon lafiyar mazauna kauyen da masu yi wa kasa hidima suka yi sannan ta yi kira ga attajiran jihar da su yi koyi da irin haka.
Mai unguwar kauyen Rugar Duka, Abubakar Lamido ya mika godiyar sa a madadin mutanen kauyen ga masu yi wa kasa hidima da jinjina musu kan wannan taimako da suka yi wa mutanen kauyukan su.