Masu hannayen jari a kamfanin mai na Oando sun yi kira da a gaggauta tsige Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun, inda suka zarge ta da shiga tsamo-tsamo a sha’anin hada-hadar kudade.
‘Yan kungiyar sun zarge Adeosun da yin katsalandan cikin harkokin Hukumar Kula da Hannayen Jarin Manyan Kamfanoni.
Shugaban Kungiyar ta masu hannayen jarin (TSAN), Muktar, tare da kodinata Taiwo Oderinde, ne suka yi wannan zargi a Legas bayan tashi daga taro, inda suka yi mata wannan kakkausan zargi.
Sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya cire minista Adeosun, su na cewa dakatar da tsohon shugaban SEC, Munir Gwarzo da kuma cire darakta-janar mai riko da ministar tayi ido-rufe, hujjoji ne da ke nuna cewa Adeosun ba ta so a binciki harkallar da ke tattare da Oando.
“Mun yi amanna da cewa cire minista Adeosun ne kadai zai tattabar wa ‘yan Najeriya cewa wannan gwamnatin da gaske ta ke yi wajen yaki da cin hanci da rashawa a kowane bangare na tattalin arzikin kasar nan.”
Discussion about this post