Malamai da kungiyoyin Addinin Musulunci, Kuji Tsoron Allah – Daga Imam Murtadha Gusau

0

Bismillahir Rahmanir Rahim

Abun bakin ciki ne da takaici ganin cewa a yau malamai sun mayar da addinin Allah siyasar dimokradiyyah, ita ma gwamnati ta biye masu a hakan. Dama ita gwamnati ba addini ne a gabanta ba. Tace ita gwamnati ce ta ba ruwan ta da addini.

Saboda haka duk wanda yazo da son zuciyar sa, za ta biye masa matukar ta hango za ya tara mata jama’ah!

A taron bikin Mauludin Shehu Ibrahim Nyass da aka gudanar a garin Kaduna Shugaba Muhammadu Buhari ya tura Minista Dambazau ya wakilce shi. A taron Mauludin Shehu Nyass a Abuja kuwa ya tura Minista Adamu Adamu ya wakilce shi.

Haka ma gwamnatin za ta yi da ace bangarorin Izala biyu ne za su yi wa’azin kasa a wurare daban-daban. Ita gwamnati babu ruwanta. An wayi gari jagororin addini da maluma suna wasa da addinin Allah, ita kuwa ta biye masu, tun da ita dama can addini ba komai bane a wurinta, shirme ne, ita kawai jama’ah take nema.

Al’amari ya kasance an koma alfahari da yawan mutane, da tara jama’ah da maganar yawa, a nuna wa ‘yan siyasa cewa fa muna da mutane don haka dole a neme mu, kuma dole ayi damu. Abun ya koma ba Allah a cikin sa. An ajiye gaskiya a gefe daya.

Kuma wannan fa ba darikar Tijjaniyyah kawai ba fa, a’a, wallahi har dukkanin bangarorin kungiyar Izala haka abin yake. Suma ayi wa’azin kasa a tara jama’ah, a gayyato ‘yan siyasa su gani. A nuna masu cewa fa 2019 dole ku neme mu! A gaba na wallahi wani malamin Izala yake alfhari da yawan su, yake cewa ai su yanzu duk wani dan siyasa dole yayi da su idan yana son cin nasara.

Suna ta wasa da rayukan talakawa, mabiyansu. Su manyan maluman suna cikin daula da sharholiya, suna cikin jin dadi su da iyalansu, suna hawa manyan motoci, suna sa tufafin kece-raini, amma suna halakar da ‘ya’yan talakawa! Sun bar talakawa cikin karuwar talauci, kunci da yunwa da rashin sanin alkibla, kuma duk da sunan addini.

Don Allah, don Allah, don Allah dan uwa kaji tsoron Allah, ka karanta wannan rubutu nawa da idon basirah, kar ka kawo wani bangaranci ko kungiyanci ko darikanci a cikin sa. Muna magana ne akan addinin Allah da aka rabe dashi ana yin ba daidai ba. Wanda kuma nasan cewa addinin Allah yafi karfin ko wace kungiya ko wata darika. Ka duba ka gani shin ba gaskiya nike fada ba?

Abin da ya kara tada mun da hankali game da wannan al’amari shine: jiya asabar na kama hanya daga Abuja zuwa Keffi a jahar Nasarawa. Wallahi idan kaga irin wahala da galabaita da cin mutunci da hadarurruka da talakawa bayin Allah suka shiga, daga Abuja zuwa Keffi bayan an tashi daga taron bukin Mauludin Shehu Nyass, za kayi kuka da bakin ciki! Idan kaga yadda aka jefa matafiya cikin kunci da damuwa da sunan addini, suna ta zage-zage, tsinuwa da Allah waddai, abun zai baka tausayi. Daruruwan talakawan da suka tafi Keffi da kafar su daga Abuja kuwa, Allah ne kadai yasan iya adadin su, saboda rashin mota. A kan wannan hanyar hadarin da ya auku jiya Allah ne kadai yasan adadin sa. An karye, an rasa rai, anyi asarar dukiyoyi, amma su manyan maluman, a lokacin da duk ake wannan, suna hotel kwancin su su da ‘ya’yansu.

Haka wannan al’amari yake a dukkanin kungiyoyin addinin Musulunci, wato: CI DA GUMIN TALAKAWA. Shi yasa sam basa so ‘ya’yan talakawa suyi karatu, su fahimci addini, su san ‘yancin su, su gane gaskiya, su san matsayin Allah da Manzonsa, su kadaita Allah shi kadai wurin bauta, su kadaita Manzon Allah shi kadai wurin biyayyah, su so Allah da Manzon sa fiye da son da za su yiwa ko wane mutum, kuma ko shi waye.

An wayi gari a yau, tsakanin ‘yan siyasa da maluman addini bamu san wa yafi wasa da hankalin talakawa ba. An wayi gari a yau, yadda wasu ‘yan siyasa ke gasa wurin tara abin duniya, sharholiya, gasar hawa manyan motoci da gasar gina manyan gidaje, haka wasu maluman addini suke yi saboda rashin tsoron Allah.

Addinin Allah ba shine a gaban su ba, a’a me zasu samu. Sun ki yarda kan al’ummah ya hadu saboda son zuciyar su, da son abin duniya. Suna ta yada karuwar rarrabuwar kai a cikin al’ummah domin wannan shine hanyar cin abincin su kuma shine hanyar samun kudin su.

Sun ki yarda su dora al’ummah a kan bin Allah da Manzonsa tsantsa, sai dai su a bisu, a bi kungiyoyin su da darikun su.

Shi yasa aka wayi gari kullun gamu nan sai rikice-rikicen addini, sai tashin hankali, sai zubar da jini, sai rashin zaman lafiya. Sai daba, sai sara-suka, sai kalare, sai matsalolin almajirai, sai ta’addanci da sauransu. Muna ikirarin mune masu addini, amma kuma matsaloli sun bi sun dabaibaye mu. Saboda bama tafiya akan ainihin addinin da Allah ya saukar wa Manzon sa, mun shigar da son rai da son zuciya a ciki. Domin babu yadda za’ayi mutum ya rike addinin Allah da gaske, sannan kuma ace yafi kowa yawan matsaloli. Ya kamata mu koma, mu duba, sannan mu gyara.

Wallahi, wallahi, wallahi za mu mutu, Allah za ya tambaye mu, kuma duk abunda muke yi Allah yana kallon mu.

Allah ya sawwake, ya shiryar damu hanya madaidaciya, amin.

Wassalamu Alaikum

Dan uwanku:

Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Najeriya. +2348038289761.

Share.

game da Author