Majalisar Tarayya ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana a gaban ta, domin yin bayani dangane da mummunan kashe-kashe da ke ta faruwa a kasar nan.
An amince da wannan roko ne, bayan da Dan Majalisa daga Jihar Kano, Bashir Baballe, dan APC, ya gabatar da rokon kudirin da Dan Majalisa daga Benuwai, Mark Gbilah, shi ma dan APC ya bagatar.
Majalisar ta amince da kudirin da Gbilah ya gabatar, a kan harin da sojoji suka kai a garin Naka, inda suka banka wa kusan rabin garin wuta, saboda matasan garin sun yi wa wani soja kisan-rubdugu.
Daga nan kuma ‘yan majalisa suka amince da cewa shugabannin hukumomin tsaron kasar nan sun kasa, kuma ba za su iya magance matsalar tsaro a kasar nan ba. Don haka sun nemi Buhari ya tsige su, a gaggauta maye gurbin su da wasu da suka cancanta.
Majalisa ta kuma jingine zaman ta na kwana uku, domin nuna jimamin su kan sa jama’ar da ake ta kashewa bagatatan a fadin kasar nan.
Sun kuma nemi gwamnatin tarayya ta shelanta cewa makiyaya masu kashe mutane su ma ‘yan ta’adda ne, kuma sun nemi a yi wa kowane makiyayi rajista.