Majalisar dattawa a zaman ta na ranar Alhamis ta dakatar da sanata Omo-Agege daga majalisar har na tsawon kwanaki 90 saboda nuna kin amincewar sa da canza jerin yadda za a gudanar da zabe a 2019.
Idan ba a manta ba majalisar tarayya ta na neman ta canza yadda za a gudanar da zabe cewa sun fi so a yi zaben su a farko kafin na shugaban kasa.
Omo- Agege ya fadi cewa wannan batu shiri ce kawai don yaki da shugaban kasa amma ba ta da wani amfani. Ya zargi majalisar tarayya din duka biyu cewa sun yi haka ne domin son kai da muzguna wa Buhari amma ba don ci gaban kasa ba.
Tun a wancan lokacin, majalisar ta mika wannan korafi da Omo-Agege yayi ga kwamin ta na da’a inda bayan ta gudanar da bincike ta ba majalisar shawara da a dakatar da sanatan na kwanaki 180. Shugaban majalisar Bukola Saraki, ya roki majalisar da suyi hakuri su sassauta masa zuwa kwanaki 90 kawai.
Omo-Agege na wakiltar Delta ta Kudu.
Discussion about this post