Mahara sun kashe mutane 15 a Coci

0

Kakakin gwamnan jihar Benuwai Terver Akase ya bayyana cewa wasu mahara da ake zargin makiyaya ne sun kashe mutane 15 a Cocin darikar Katolika dake da suna St Ignatus a Jihar.

Akase ya bayyana cewa maharan sun far wa mutanen ne a daidai suna bauta da safiyan Talata a kauyen Ayar-Mbaloma dake karamar hukumar Gwer na gabas.

” Maharan sun kashe limaman cocin biyu Joseph Gor da Felix Tyolaha da wasu mutane 13.”

Sai dai kuma har yanzu kwamishinan ‘yan sandan jihar Fatai Owoseni ko kuma kakakin ‘yan sandan, Moses Yamu basu ce komai ba a kai.

Share.

game da Author