Mahara sun kashe masu hako ma’adinai a jihar Zamfara

0

Mahara sun kai wa kauyuka biyu hari a karamar hukumar Anka dake jihar Zamafara inda mutane da dama suka rasa rayukan su sanadiyar harin.

Wani wanda harin ya faru a idon sa mai suna Sadi Musa ya ce harin ya auku ne ranar Laraba inda wasu ‘yan bindiga suka kai hari wurin da ake hako ma’adinai a kauyen Kuru-Kuru dake karamar hukumar Anka.

” Mutane da dama sun rasa rayukan su sanadiyyar harin da ‘yan bindigan suka yi a filin hako ma’adinan.”

Musa ya ce washe gari kuma maharan sun sake kashe mutane yayin da suke jana’izan wadanda suka kashe a filin hako ma’adinai a makabartan dake kauyen Jarkuka.

Jami’in harka da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Mohammed Shehu ya tabbatar da hakan amma ya ce bashi da masaniyar adadin yawan mutanen da suka mutu.

Ya ce wannan ba shine karo na farko ba da irin haka ke faruwa a karamar hukumar Anka ba domin makomi biyu da suka wuce wasu maharan sun far wa mutane a kauyen Bawan Daji inda akalla mutane 30 suka rasa rayukan su.

Share.

game da Author